Taba Ka Lashe: 29..07.2020

Published: Aug. 4, 2020, 12:58 p.m.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne, alumar Musulmi a fadin duniya suka fara shagulgulan babbar Salla ko kuma Sallar layya. To sai dai a bana bikin ya zo ne daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da annobar corona da ta janyo koma baya a bangarori dabam-dabam na rayuwa.