DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019)

Published: Feb. 13, 2019, 1:50 p.m.

DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019) [1][2]\n

Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba.

\n
    \n
  1. Host: Munta Gayuwa*
  2. \n
  3. Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin ta\u0199aici na roman baka da 'yan siyasar \u0199asar ke yi musu, tsawon shekaru da \u0199asar ta kama mulki irin na demokra\u0257iya. Toh wane irin al\u0199auran ne wadannan 'yan siyasa ke yi wa wadannan mutane na karkara?"In mun ci za\u0253e, za mu yi muku hanya. In mun ci za\u0253e, za mu kawo muku wuta, asibiti, da sauran abubuwa. Amma ko \u0257aya, ba wanda ya ta\u0253a cika mana. Wani pole-waya an kafa a nan ya kai har shekara goma sha biyu (12), amma wallahi ba a zo yin komai ba!"
  4. \n
  5. Nigeria: Muna tafe da rahoto kan wannan matsala. Hakannan kuma za'a ji al'ummar Fulani da dokar hana kiwo ta shafa a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriyar. Sun bu\u0199aci kariya ne daga jami'an tsaro a duk inda suke don basu damar za\u0253e kamar sauran 'yan \u0199asar Najeriyar.
  6. \n
  7. World Radio Day 2019: Yayin kuma da ake ranar rediyo ta duniya, za mu ji yadda wasu al'ummomi ke bayyana mahimmancin kafarta sadarwa a garesu.
  8. \n
  9. Morocco: Hukumomi a \u0199asar Morocco, sun kama wasu Faransawa da suka ce suna \u0257aukar nauyin \u0199ungiyar nan ta IS.
  10. \n
  11. Nigeria: Mutane da dama sun mutu lokacin gangamin ya\u0199in neman za\u0253e na shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya.
  12. \n
  13. Thailand: Wasu fursunoni, wato 'yan \u0199abilar Uyghir, sun tsere daga hannun jami'an tsaro a \u0199asar Thailand.
  14. \n