Published: Feb. 10, 2019, 1:51 p.m.
BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019 [10][11]\n
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
\n
\n - Hosts: Ibrahim Mijinyawa
\n - Nigeria Elections 2019: Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP (the major opposition party), ta yi zargin cewa an hana ta gudanar da gangamin ya\u0199in neman za\u0253e a Abuja.Har mun tura mutanen mu wa\u0257anda za su je su shiya mana wurin tsayawa a yi magana (podium)... sai aka ce musu wannan wuri ba za a ba mu shi ba. Don haka sai dai mu nemi wani.
\n - Chad: Rundunar sojin Cadi kuwa, ta ce ta kama 'yan tawaye da dama da suka tsallaka cikin \u0199asar daga kudancin Libya bayan artabun da aka yi da su a arewacin \u0199asar.
\n - Ethiopia: Tsofaffin 'yan tawaye ne sama da dubu guda suka mi\u0199a da makamansu bayan wata yarjejeniya da aka \u0199ulla da su da gwamnatin \u0199asar.
\n